16 Mayu 2020 - 06:38
Kasashen Rasha Da China Sun Yi Watsi Da Bukatar Tsawaita Takunkuman Makamai Kan Iran

Kasashen China da Rasha wadanda suke da kujerun din din din a kwamitin tsaro na MDD sun yi watsi da batun kara tsawaita takunkuman saya da seyar da makamai kan kasar Iran wanda ya zo cikin kudurin kwamitin tsaro na majalisar bai lamba 2231.

(ABNA24.com) Kasashen China da Rasha wadanda suke da kujerun din din din a kwamitin tsaro na MDD sun yi watsi da batun kara tsawaita takunkuman saya da seyar da makamai kan kasar Iran wanda ya zo cikin kudurin kwamitin tsaro na majalisar bai lamba 2231.

Jakadan kasar China a majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na kasar Amurka ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ba ta da hurumin sauya wani abu a cikin kuduri mai lamba 2231 ballandata na ta tsawaita takunkuman da kudurin zai daukewa Iran a karshen watan Ocotaba na wannan shekara.

Jakadan ya kara da cewa ficewar kasar Amurka daga yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015 ya tabbatar da gazawarta wajen cika alkawuran da ke cikin yarjejeniyar.

Har’ila yau ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergay Labrov yana cewa gwamnatin Amurka ba za ta iya tsawaita takunkuman makamai kan Iran wanda ya zo cikin kuduri mai lamba 2231 ba saboda ba zai yu a dabbaka wani bangare na kudurin sannan a bar wani bangare ba.



/129